Najeriya ta siya sabbin jiragen yaki don kawar da Boko Haram - AM Saddique

Najeriya ta siya sabbin jiragen yaki don kawar da Boko Haram - AM Saddique

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da manyan hafsoshin hukumar Sojin Najeriya da shugabannin hukumomin tsaro gabanin tafiyarsa Landan a ranar Juma'a, 17 ga Junairu, 2020.

Bayan ganawar, shugaban mayakan saman Najeriya, Sadique Abubakar, ya bayyanawa manema labarai cewa sun tattauna kan abubuwa da dama kuma ana samun nasara.

AM Sadique ya ce hukumar ta sayi jirage masu saukan angulu biyu domin yakan yan ta'adda da yan bindiga a yankin Arewa maso yamma.

"Wasu Makaman (da akayi oda) sun fara isowa. A wajen mayakan sama, jiragen yaki masu saukar angulu biyu sun iso ranar 15 ga Junairu kuma muna kan shiryasu yanzu."

Najeriya ta siya sabbin jiragen yaki don kawar da Boko Haram - AM Saddique
Najeriya ta siya sabbin jiragen yaki don kawar da Boko Haram - AM Saddique
Asali: UGC

Najeriya na fama da rashin tsaro a kusan dukkan sassan jihar. Wadannan sun hada da Boko Haram da ISWAP a Arewa maso gabas, yan bindiga da masu garkuwa da mutane a yankin Arewa maso yamma da kuma yan bindiga makiyaya a kudu maso yamma.

Mun kawo muku rahoton cewa Akalla mutane 30 suka rasa rayukansu yayinda akayi awon gaba da 100 lokacin da yan bindiga suka budewa motoci wuta a babbar titin Kaduna zuwa Zariya a ranar Talata, 15 ga Junairu.

Hukumar yan sandan jihar, a jawabin da ta saki ta bayyana cewa yan bindigan sanye da kayan Sojoji sun kai harin ne misalin karfe 11 na dare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel