Dan majalisar Kano ya dauki nauyin dalibai 100 don karatu a kasar Sudan da Indiya
Tsohon hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan harkokin watsa labaru ta rediyo, Sha’aban Ibrahim Sharada ya dauki nauyin dalibai 100 domin su yi karatun digiri a kasar Sudan da Indiya.
Legit.ng ta ruwaito wannan labari ya bayyana ne a shafin kafar sadarwar zamanin Sha’aban Ibrahim Sharada sabon shafi, wanda ke wakiltar mazabar birnin Kano a majalisar wakilan Najeriya.
KU KARANTA: Badakalar satar N200m: Jami’an EFCC sun yi awon gaba da akawun majalisa, matarsa da yaransa 2

Asali: Facebook
Adadin daliban da suka samu dacewa da wannan kabakin arziki na Sharada sun kai mutum 100, kuma sun hada da dalibai da dalibai mata, anyi bikin sallamar yaran ne a fadar gwamnatin jahar Kano, inda gwamnan jahar, Abdullahi Umar Ganduje da kansa ya samu halarta.
A jawabinsa, Gwamna Ganduje ya dauki alkawarin Inganta harkar Ilimi a jahar Kano ta hanyar kirkirar Ilimi kyauta a matakin Firamari, kuma ya yi yabo da jinjina ga Sha'aban Sharada, har yake mamakin irin ayyukan da yake yi.

Asali: Facebook
“Na yi matukar farin ciki da ganin matasa a cikin wannan tafiyar taka domin matasa sune al'umma duk wani abu da kake nema to ka nemi matasa, idan ma zabe kake son ci to ka nemi matasa, nayi matukar farin ciki da naga tafiyarka ta matasa ce da.
"Kuma yadda naga kana tallafawa Mata, don haka zamu cigaba da karfafa maka gwiwa ta kowacce hanya domin ka cigaba da gudanar da abubuwan da ka saba” Inji shi.
Daga karshe Ganduje ya yi kira ga al'ummar karamar hukumar birni da su kara rike wannan bawan Allah hannu bibbiyu domin kuwa sun yi dace kwarai, sa’annan ya yi addu’ar Allah Ya jikan mahaifinsa kuma Allah Ya kara yi masa Albarka.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng