Yanzu-yanzu: Sai da na taka cikin daji na tsawon sa'o'i biyu - Sarkin Potiskum yayi jawabi bayan harin yan bindiga

Yanzu-yanzu: Sai da na taka cikin daji na tsawon sa'o'i biyu - Sarkin Potiskum yayi jawabi bayan harin yan bindiga

- Sarkin Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya, ya bayyana yadda ya tsallake rijiya da baya a harin yan bindiga ranar Juma'a, 17 ga watan Junairu

- Sarkin ya ce sai da ya kwashe sa'o'i biyu yana takawa cikin daji bayan harin

- Sarkin ya yi kira ga yan Najeriya su taimakawa gwamnatin tarayya wajen yaki da yan ta'adda

Sarkin Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya, ya bayyana yadda ya tsallake rijiya da baya a harin yayi sanadiyar mutuwar mutane 30 a hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Bayan sallamarsa daga asibiti da yayi jinya kwana biyu a Kaduna, Sarkin ya bayyana cewa sai da taka na sa'o'i biyu cikin daji.

Ya yi alhinin fadawansa hudu da suka rasa rayukansu a harin kuma ya mika godiyarsa ga yan sandan da suka taimakawa wajen cetonsa.

Mun kawo muku rahoton cewa Akalla mutane 30 suka rasa rayukansu yayinda akayi awon gaba da 100 lokacin da yan bindiga suka budewa motoci wuta a babbar titin Kaduna zuwa Zariya a ranar Talata, 15 ga Junairu, Premium Times ta ruwaito.

Hukumar yan sandan jihar, a jawabin da ta saki ta bayyana cewa yan bindigan sanye da kayan Sojoji sun kai harin ne misalin karfe 11 na dare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel