Yanzu-yanzu: Na yi tafiya a kafa na sa'o'i biyu bayan harin Boko Haram - Sarkin Potiskum

Yanzu-yanzu: Na yi tafiya a kafa na sa'o'i biyu bayan harin Boko Haram - Sarkin Potiskum

Sarkin Potiskum, Mai martaba Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya ya yi magana a kan harin da 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram suka kai masa inda hudu daga cikin hadimansa suka rasa rayyukansu a ranar Talata.

Ya ce ya yi tafiya a kafa na kimanin sa'o'i biyu a cikin daji domin ya tsira da ransa yayin harin da 'yan ta'addan suka kai wa tawagarsa a kan hayar Kaduna zuwa Zaria.

Sarkin ya mika godiyarsa ga Allah da ya kubutar da shi da sauran hadimansa daga harin bayan ya koma fadarsa a Potiskum na jihar Yobe daga asibiti a Kaduna inda aka kai shi likitoci suka duba shi.

DUBA WANNAN: Safarar yara: 'Yan sanda sun kama Farfesa a Kano

Sai dai duk da haka sarkin ya yi bakin cikin rasuwar hudu daga cikin hadimansa tare da daya da har yanzu ba a san inda ya ke ba.

Sarkin da ya yi magana da wakilin The Nation a fadarsa da ke Potiskum ya yi kira da dukkan mutane su goyi bayan gwamnatin tarayya don samar tsaro a kasar.

Ku biyo mu don karin bayani ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel