An garmake Limanin da aka aurawa namiji a matsayin mace a Kurkuku

An garmake Limanin da aka aurawa namiji a matsayin mace a Kurkuku

Sheikh Mohammed Mutumba, Limamin Masallacin Kyampisi Masjid Noor, wanda ya auri namiji ya gurfana a gaban kotu bayan an zargeshi da laifin kwanciya da namiji kuma an garkameshi a Kurkuku.

Yayinda ya bayyana gaban kotun Kayunga a ranar Alhamis, Alkalin kotun, Irene Akello, ta ce sai an kai Limanin babban kotu kafin a bashi daman yin magana.

An gurfanar da Sheikh Mutumba ne tare da katon da aka aura masa a matsayin amce, Richard Tumushabe da akafi sani da Swabullah Nabukeera.

An tuhumci Sheikh Mutumba da Swabullah da aikata laifin a watan Disamban, 2019.

An dage karar zuwa ranar 24 ga Juaniru domin cigaba da sauraron karar.

Mun kawo muku rahoton cewa Sheikh Mohammed Mutumba babban limamin masallacin Kyampisi ne dake Uganda wanda ya gano amaryarsa katon gardi ce.

Ma'auratan basu taba kwanciyar aure ba kuma sunyi makonni biyu da aure amma amaryar tace tana jinin al'ada ne.

Mutumba yace, bayan matarsa tayi ikirarin cewa tana jinin al'ada, ya hakura tare da jiran har jinin ya dauke.

Amma kuma sa'ar Nabukeera ta kare ne bayan makwabcin Mutumba yayi ikirarin cewa sabuwar amaryar Mutumba ta tsallake katanga tare da satar masa talabijin da kayan sanyawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel