Kara da kiyashi: Yadda wani mutumi ya kashe abokinsa har ya cinye marainansa

Kara da kiyashi: Yadda wani mutumi ya kashe abokinsa har ya cinye marainansa

Dole ne jama’a su dinga addu’a Allah Ya rabasu da mugayen abokai, wadanda basu da burin ganin cigabansu sai dai kokarin ganin mugun abu ya samesu, anan bama fatan mugun abu ya samu aboki aka yi ba, a’a, wani Kura ne da fatan Akuya ya kashe abokinsa.

Kafar sadarwa ta WILD ta bayar da labarin wani mutumi dan shekara 50 mai suna Mark Latunski da jami’an rundunar Yansanda suka kama shi bayan ya kashe wani sabon abokinsa, matashi dan shekara 25 mai suna Kelvin Beacon.

KU KARANTA: Duk shugaban da aka yi a Najeriya sai yan Najeriya sun zage shi, me yasa? – John Oyegun

Kara da kiyashi: Yadda wani mutumi ya kashe abokinsa har ya cinye marainansa
Mark da Beacon
Asali: Facebook

Rahotanni sun bayyana cewa an fara neman Beacon ne tun bayan bacewarsa a ranar Kirismeti, ranar daya fita, daga nan bai sake dawowa ba, daga nan aka fara sanar da cigiyarsa.

Majiyar ta bayyana cewa abokan biyu sun fara haduwa ne ta shafukan yana gizo, a haka suka shirya inda zasu hadu domin su gana a karon farko, amma daga nan sai Mark ya ja Beacon zuwa gidansa dake Michigan, inda ya kashe shi, ya rataye shi a katakon rufin gidansa.

A wannan hali jami’an Yansanda suka tarar da gawar Beacon a lokacin da binciken neman Beacon ya fadada har zuwa gidansa, ganin haka yasa Marka ya amsa laifinsa, inda yace ya kashe Beacon ne da wuka, sa’annan ya yanke masa maraina da wuka ya cinye duk.

A yanzu haka Yansandan Michigan na tuhumar Mark da aikata laifuka biyu da suka hada da kisan kai tare da cin naman mutum, game da hukuncin da kotu za ta yanke masa sai yadda hali ya yi.

Sai dai wata majiya daga rundunar Yansandan jahar ta bayyana cewa ta taba samun kira daga wasu jama’a dake makwabtaka da Mark cewa sun hangi wani matashi ya fito daga gidansa a guje cikin halin tsoro da firgici, a watan Nuwamba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng