Duk shugaban da aka yi a Najeriya sai yan Najeriya sun zage shi, me yasa? – John Oyegun

Duk shugaban da aka yi a Najeriya sai yan Najeriya sun zage shi, me yasa? – John Oyegun

Tsohon shugaban jam’iyyar APC, Cif John Odigie Oyegun ya bayyana cewa tsarin mulkin dimukradiyya ya tabbata a Najeriya, tamkar takalmin kaza, mutu ka raba. Sai dai ya koka kan yadda yan Najeriya basa jin dadin tsarin.

Oyegun ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi a taron tattaunawa da kamfanin jaridar Daily Trust ta shirya karo na 17 a babban birnin tarayya Abuja, mai taken “Shekara 20 da dimukradiyya a Najeriya: Karfinmu, rauninmu da damarmakinmu.’

KU KARANTA: Nan bada jimawa ba gwamnatin Najeriya za ta tura wakilinta zuwa duniyar wata

Oyegun ya bayyana cewa tun bayan dawowar dimukradiyya kimanin shekaru 20 da suka gabata ba’a taba samun wata gwamnati ba face yan Najeriya sun yi fushi da ita. “A ra’ayina, ina da yakinin dimukradiyya ta samu gindin zama a Najeriya.

“Ina da yakinin yan Najeriya sun gamsu da amsan nasara ko faduwa ta hanyoyi daban daban, kodai ta hanyar hukuncin kotun koli ko kuma ta bin misalin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan daya amsa shan kayi.

“Sai dai abin dake damu na shi ne barazanar da dimukradiyyarmu take fuskanta, bari na ari maganan da tsohon gwamnan jahar Borno ya yi, inda yace dole ne mu tabbata Najeriya ta yi aiki, menene dalilin da yasa Najeriya bata aiki?” Inji shi.

Tsohon gwamnan na jahar Edo ya bayyana cewa “Bamu taba tambayar kanmu me yasa jama’a ke jin haushin gwamnoninsu kafin su bar mulki a cikin shekaru 20 da muka yi na siyasa, me yasa suke kara talaucewa, me yasa suke gajiya da shuwagabannin, wadannan tambayoyin kadai barazana ne ga dimukradiyyan mu, saboda a yau mun fara jin gunagunin da bamu saba ji a baya ba.

“Amotekun na daga cikin ire iren gunagunin nan, wanda ya nuna akwai abin da jama’a suke so a yi musu a wasu fannoni amma an gaza sama da shekaru 20. Ko ni ban zan amsoshin tambayoyin nan ba, sai dai wani taron tattaunawar ya amsa su.” Inji shi.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Sule Lamido, Namadi Sambo, tsohon shugaban kasar Botswana, Festus Mogae, Gwamna Kayode Fayemi, Ibrahim Shehu Shema, Kashim Shettima, Attahiru Bafarawa da sauransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel