An kama sojan da ya kashe mai sayar da takalma a Kaduna

An kama sojan da ya kashe mai sayar da takalma a Kaduna

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna sun tabbatar da kama wani jami'in soja da aka ce ya kashe wani mai sayar da takalma a Kaduna.

Mai magana da yawun 'yan sandan, DSP Yakubu Sambo ya tabbatarwa Daily Trust labarin inda ya ce tuni an kama sojan kuma yana hannun 'yan sanda.

Sabo ya ce wanda ake zargin ya suma kafin 'yan sanda suka kai shi asibiti sai dai har yanzu ana neman sauran mutanen da suka aikata mummunan aikin tare da shi.

"Yan sanda sun kai shi asibiti saboda ya suma. Yanzu haka yana hannun mu kuma jami'an mu suna cigaba da farautan sauran abokansa uku," inji shi.

A baya, mun ruwaito muku cewa an samu yamutsi da kasuwan Sheikh Gumi da ke Kaduna inda wasu fusatattun matasa suka yi wa wani soja duka da aka ce ya daba wa wani mai sayar da takalmi wuka.

DUBA WANNAN: Hotunan ziyarar da Ahmed Musa da 'yan kungiyarsa suka kai wa yariman Saudiyya

Wadanda suka shaida faruwar lamarin sun ce sojan da ke sanye da kayan farar hula a lokacin ya dauki matakin ne bayan musayar maganganu da suka yi a kasuwar.

Ba a san tabbbacin abinda ya haifar da cacan bakin tsakaninsu ba amma lamarin ya faru ne misalin karfe 2.30 na rana a Royal a kasuwan.

Wani da abin ya faru a idonsa mai suna Salis, ya ce 'yan banga ne suka ceci mutumin da ya yi ikirarin shi soja ne kafin 'yan sanda su iso wurin.

Ya ce, "Sojan ne ya dabawa mai sayar da takalman wuka a kirji bayan sun yi musayar maganganu sannan wasu matasa da ke wurin sun yi wa sojan rauni a kai kafin a cece shi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel