Ya kashe matarsa da 'ya'yansa guda uku ya kulle kanshi dasu a daki na tsawon mako uku

Ya kashe matarsa da 'ya'yansa guda uku ya kulle kanshi dasu a daki na tsawon mako uku

- Anthony Todt mazaunin Florida ya bar makwabta baki bude bayan ganowa da aka yi ya kashe matarshi, 'ya'yansu uku da karensu

- Todt ya cigaba da rayuwa da gawawwakin iyalan nashi har zuwa lokacin da 'yan sanda suka bankado

- Ana zargin shi da kisan ne saboda tsabar bashin da ake bin shi wanda ya kai $100,000

Wani magidanci ya saka mutane cikin tsananin mamaki bayan da ya amsa laifin shi na kisan matar shi, yaransu uku da Karen shi kuma ya cigaba da zama tare da gawawwakinsu har na tsawon makonni biyu kafin ya shiga hannun 'yan sanda.

Anthony Todt, matar shi ta shekaru 20 mai suna Megan, yaransu uku, Alex, Tyler da Zoe duk sun bace ne kamar yadda makwabtansu suka bayyana.

Makwabtansu sunce basu ganinsu tun tsakiyar Disamba kuma 'yan uwansu basu ji daga garesu ba tun ranar 6 ga watan Janairu.

Amma 'yan sanda sunce Todt mai shekaru 44 na bada amsar sakonnin da 'yan uwa da abokan arziki ke tura musu a yayin da yake rayuwa da gawawwakinsu.

An gano cewa wasu suna bin Todt bashin $100,000, ana gab da korarshi daga gidan haya saboda bai biya ba kuma wata cibiyar tarayya na zargin shi da damfara a wani kasuwanci.

Ta yadda suka mutu ne har yau ba a sanar da mutane ba. Amma an yadda cewa sun rasu ne wajen karshen watan Disamba.

KU KARANTA: Mijina da yayi mini ciki sai ya gudu, baya dawowa har sai yaji cewa na haihu - Rukayya

Wani dan sandan yankin mai suna Sheriff Russ Gibson a ranar Laraba yace: "Zan iya cewa ofishinmu ya samu wani kira daga 'yan uwansu a ranar 29 ga watan Disamba da bukatar a duba su saboda an sanar da ita cewa suna zazzabi kuma basu ji daga garesu ba na kwanaki biyu."

Yace hukumomi sun kai ziyara gidan amma basu shiga ciki ba saboda tamkar ba kowa.

Amma kuma hankulansu bai tashi ba saboda Todt ya saba yin mako daya baya gida sakamakon yanayin kasuwancinsa. 'Yan sandan basu zargi komai ba.

Sun koma gidan Todt ne a ranar Litinin bayan wani makwabcinsu ya kira jami'an. Sun samu damar shiga gidan inda suka tarar da gawawwakin 'yan gidan.

A take kuwa aka kama Todt wanda aka mika asibiti saboda ya sha wata kwaya wacce ta gusar mishi da hankali. Bayan kammalawa da asibiti, an mika Todt gidan yari kafin a fara shari'ar shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel