Kotu ta daure mutane 4 tsawon shekaru 7 a kurkuku saboda satar taliya da sigari

Kotu ta daure mutane 4 tsawon shekaru 7 a kurkuku saboda satar taliya da sigari

Wata babbar kotun jahar Ekiti dake zamanta a garin Ado Ekiti ta yanke ma wasu mutane hudu hukuncin daurin shekaru bakwai bakwai a gidan gyara hali bayan kamasu da laifin satar taliyar Indomie da sigari.

Jaridar Vanguard ta ruwaito Alkalin kotun mai sharia Bamidele Omotosho ne ya yanke wannan hukunci mai tsauri a kan matasan hudu da suka hada da: Owoeye Ojo, Agbetuyi Taiwo, Adeniyi Busayo da Lasisi Friday.

KU KARANTA: Wani dalibi ya datse dan yatsan hannun abokinsa a rikicin makaranta

Alkalin yace ya kamasu ne da laifin fasa shago tare da kutsa kai cikinsa inda suka kwashi taliyar Indomie da sigari, kamar yadda suka tabbatar ma kotu wajen amsa laifukansu, don haka Alkalin ya hanasu damar biyan tara.

Tun da fari, sai da lauya mai kara, Wale Fapohunda ya bayyana ma kotun cewa mutanen sun aikata laifin ne a ranar 26 ga watan Agustan shekarar 2017 a unguwar Enu Odi, Odo-Ado cikin garin Ado Ekiti, inda suka fasa shagon Iyabo Oge da tsakar dare, tare da mata sata, laifin daya saba ma sashi na 413 da 516 na kundin hukunta manyan laifuka.

Lauya mai kara ya gabatar da shaidu guda 3 a gaban kotu, sa’annan ya gabatar da hujjoji da suka hada da hotuna, shaidun gani da ido, jawaban da wadanda ake tuhuma suka bayar da kuma kayan da suka sata.

Shi kuwa a nasa bangaren, lauyan wadanda ake kara, Yinka Opeleye da Adekunle Ojo sun gabatar da shaidu biyu ne kacal a gaban kotun, sa’annan suka rokan ma mutanen alfarmar sassauci daga kotun sakamakon wannan ne karo na farko da suka aikata laifin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel