Nan bada jimawa ba gwamnatin Najeriya za ta tura wakilinta zuwa duniyar wata

Nan bada jimawa ba gwamnatin Najeriya za ta tura wakilinta zuwa duniyar wata

Ministan kimiyya, fasaha da kirkirekirkire a Najeriya, Ogbonnaya Onu ya jaddada muhimmancin ilimin kimiyya da fasaha da kere kere ga cigaban kasa, sa’annan ya tabbatar da manufar gwamnatin Najeriya na tura wakilanta zuwa duniyar wata.

Minista Onu ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi a taron kungiyar tsofaffin daliban Izzi da ya gudana a tsangayar ilimi na jami’ar jahar Ebonyi (EBSU) reshen Ishieke, inda yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara ma bangaren kimiyya da fasaha karfi domin ta jagoranci aikin karkatar da akalar tattalin arzikin Najeriya.

KU KARANTA: Wani dalibi ya datse dan yatsan hannun abokinsa a rikicin makaranta

“Ban ji dadin yadda bayan an kammala rera taken Najeriya sai na ji dalibai suna ta bayyana irin aikin da suke su yi idan sun girma, amma ban ji mutum daya ya ce yana son zama Injiniya ba, ya kamata shugaban makaranta ya gayyaci kwararru domin su fahimtar da dalibai muhimmancin ilimin kere kere ga cigaban kasa.

“Abin takaici ne idan aka yi wayi gari babu dalibi ko daya daga makarantar nan da ya zama Ininiya saboda a matakin gwamnatin Najeriya mun fara tsare tsaren yadda zamu aika mutane duniyar wata.

“Tabbas muna da wannan tsari, kada ka taba tunanin ba zai yiwu ba, watakila ya dauki shekara 20, ko 30, amma muna da wannan tsari, kuma zan yi farin ciki idan aka samu dalibi daga wannan makarantar ya shiga duniyar wata, sai dai hakan ba zai yiwu ba sai da ilimin kimiyya da fasaha.

“Akwai damarmaki da dama da muke zubarwa a kasar nan, kuma wata matsala da muke fama da ita ita ce mun saki tattalin arzikin mu ga kayan saye da sayarwa kadai, da farko mun fara da kayan noma, zuwa danyen mai da iskar gas ba tare da sun kara mana komai ba.” Inji shi.

Daga karshe ministan ya yi kira ga tsofaffin dalibana makarantar da suka samu nasara a fannoni daban daban da su tabbata sun waiwayi makarantar domin tallafa mata ta yadda martabarta za ta dawo.

A nasa bangaren, ministan ya tallafa ma makarantar da kayan gwaje gwaje na kimiyya, kwamfuta guda 12 da kuma littafan karatu 12 wanda ministan da kansa ya wallafa a fannoni daban daban.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel