Gwamnati na shirin samarwa talakan Najeriya wani salon man fetur a farashin N97

Gwamnati na shirin samarwa talakan Najeriya wani salon man fetur a farashin N97

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin samar da wani sabon salon man fetur mai suna Compressed Natural Gas (CNG) - domin talaka ya samu saukiN mai a farashin N95 zuwa N97 ga lita.

Hakazalika gwamnati ta yi alkawarin cewa za'a tabbatar da dokar kamfanin man fetur PIB kafin ranar 29 ga Mayun, 2020.

Karamin ministan arzikin man fetur, Cif Timipre Sylva, ya bayyana hakan ne ga manema labarai ranar Alhamis a Abuja.

Yayinda aka tambayeshi shin gwamnati zata rage farashin man fetur domin talaka ya samu sauki, ministan ya ce ana shirin samar da wani sabon kalan man fetur da zai maye na yanzu kuma mafi rahusa.

Ya bayyana cewa an gwada amfani da man CNG a garin Benin City cikin motoci 10,000 kuma har yanzu suna amfani da shi.

KU KARANTA: APC ta hada baki kotun koli don baiwa APC jihar Bauchi, Sokoto, Adamawa da Benue

A cewarsa: "Shawarar da muka yanke shine mu yi kokarin samawa jama'a wani mafita. Shi yasa zamu koma amfani da CNG.

"Misalin motocin Sufuri, CNG ya fi man feturin yanzu arha. Sabanin N145 bayan kudin tallafi, CNG zai samu a farashin N95 zuwa N97."

Ministan ya bayyana cewa yan Najeriya ba zasu sake fuskantar karancin man fetur ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel