APC ta hada baki kotun koli don baiwa APC jihar Bauchi, Sokoto, Adamawa da Benue

APC ta hada baki kotun koli don baiwa APC jihar Bauchi, Sokoto, Adamawa da Benue

Kwamitin gudanarwan jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP, ta bayyana cewa jam'iyyar ta samu rahoton leken asiri cewa jam'iyyar All Progressives Congress, APC, na shirin amfani da kotun koli wajen kwace jihohin PDP.

Shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus, ya bayyana hakan ne a hira da manema labaran da yayi a ranar Alhamis inda ya ce juyin mulki kotun koli ta yiwa jam'iyyarsa a jihar Imo.

Saboda haka, Uche Secondus, ya ce daukacin shugabanni da mambobin jam'iyyar PDP basu amince da shugaban Alkalan Najeriya, Tanko Muhammad, ba, musamman a shari'ar jihohin Kano, Sokoto, Benue, Bauchi Adamawa, Plateau da sauransu.

A cewar Secondus, Alkali Tanko Mohammad, ya zubar da mutuncinsa kuma yan Najeriya sun daina ganin girmansa.

KARANTA WANNAN Yan bindiga sun hallaka mutane 29 a jihar Zamfara

Secondus yace: "Mun samu rahoton leken asiri kafin shari'ar jihar Imo cewa wasu jigogin APC sun shirya amfani da kotun koli wajen kwace jihohin PDP irinsu Imo, Sokoto, Bauchi Adamawa da Benue."

"Maganar gaskiya ita ce, kotun koli karkashin Alkali Tanko Mohammad, ta zubar da mutuncinta kuma yan Najeriya sun daina ganin girmanta."

"Ya canza kwamitin Alkalai sau uku saboda duk Alkalin da bai amince da kisan demokradiyyan da suke shirin yi ba, sai CJN (Tanko Muhammad) ya canza shi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel