Yan bindiga sun hallaka mutane 29 a jihar Zamfara

Yan bindiga sun hallaka mutane 29 a jihar Zamfara

Akalla mutane 29 sun rasa rayukansu a harin da wasu yan bindga suka kai kauyen Babban Rafi dake karamar hukumar Gummi, ta jihar Zamfara. Punch ta ruwaito.

Wani mai idon shaida wanda haifaffen dan kauyen ne, Malam Musa Ibrahim, kuma ya tsallake rijiya da baya ya bayyanawa manema labarai cewa yan bindigan sun dira kauyen ne da safiyar ranar Talata kan babura dauke da bindigogi AK47.

A cewarsa, yan bindigan na dira cikin garin suka fara harbin kan mai uwa da wabi inda mutane da dama suka hallaka, yayinda wasu suka tsira.

Musa ya kara da cewa yan bindigan sun bibiyi wadanda suka gudu kuma suka kashe su.

Ya ce yan bindigan sun yi awon gaba kayan abinci da daddodbi bayan fitittikan mutane daga kauyen.

Bayan harin, mutan garin sun ci birne mutane 21 yan gari, bayan wasu gawawwakin baki takwas da ba'a birne ba tukun.

Yace: "Ina cikin wadanda suka gudu cikin daji. Na tsallaka rijiya da baya ne don na hau saman bishiyan da ba za'a iya ganina ba."

"Mun birne gawawwaki 21 saboda yan gari ne amma mun bar wasu gawawwaki takwas saboda baki ne da suka zo daga jihar Neja."

Musa ya kara da cewa da yiwuwan mutanen da aka kashe sun fi haka "saboda har yanzu akwai wadanda basu dawo gida ba kwanaki biyu yanzu."

Amma kakaki hukumar yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu ya bayyana cewa mutane 14 kadai aka kashe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel