Kudin yanka: Malami ya damfari mabiyansa N4.3m

Kudin yanka: Malami ya damfari mabiyansa N4.3m

Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta gurfanar da wani malami mai suna Kabiru Adabayo gaban kotun majistare ta jihar Legas a kan zarginsa da ake da damfarar wani mabiyi mai suna Oluwadamilola Oyesomi naira miliyan hudu da dubu dari uku.

An gano cewa Kabiru ya karba makuden kudaden ne daga wajen mutumin, da sunan zaiyi wata yanka.

Jaridar The Punch ta gano cewa an zargi Kabiru da karbar kudaden daga wajen Oyesomi ne a shekaru biyu da suka gabata. Ya kuma waskar da kudin ne don amfanin kansa kuma ya bace a lokacin da ya gano 'yan sanda na nemansa.

A ranar Laraba ne aka gurfanar da Kabiru sakamakon zarginsa da ake yi da laifuka biyu da suka hada da damfara da kuma sata a gaban Alkali Olufunke Sule-Amzat.

Ya musanta zargin da ake yi masa.

DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa ta ce za ta binciki gwamnonin da suka yi ruf-da-ciki da kudaden kananan hukumomi

Dan sanda mai gabatar da kara mai suna Ben Emuerhi, ya bayyana cewa an kama Kabiru ne bayan shekara daya da aikata laifin. Ya yi wannan damfarar ne tun a watan Disamba na 2018 a Pen-Cinema dake yankin Agege na jihar Legas.

Kamar yadda dan sandan ya sanar, laifukan sun ci karo da sashi na 280 sakin layi na 1 da kuma sashi na 314 sakin layi na 2 na dokokin laifukan jihar Legas.

Sule-Amzat ta bada belin wanda ake zargin a kan kudi naira dubu dari biyar tare da tsayayyu biyu. Ta dage sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Fabrairu na 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel