Wani dalibi ya datse dan yatsan hannun abokinsa a rikicin makaranta

Wani dalibi ya datse dan yatsan hannun abokinsa a rikicin makaranta

Rikici ya kaure tsakanin wasu daliban makarantar sakandari a birnin Yaounde na kasar Kamaru, inda wani dalibi cikin fushi ya dauki adda ya sare dan yatsan abokinsa da dalibi a cikin aji.

BBC Hausa ta ruwaito sunan dalibin da aka datse mai yatsa Anaud Alexandre Mbappe, yayin da ta sakaya sunan dalibin daya tafka masa wannan aika aika, sai da tace lamarin ya auku ne a garin Obala dake makwabtaka da Yaounde.

KU KARANTA: Karamin yaro dan Fulani makiyayi ya gamu da ajalinsa a hannun miyagu a Kaduna

Shaidun gani da ido sun tabbatar da aukuwar lamarin, inda suka ce sabani aka samu tsakanin daliban biyu, amma ba tare da wata wata ba shi wannan dalibi sarkin fushi ya dauko adda ya illata Alexandre.

Idan za’a tuna mun kawo rahoton wani dalibin sakandari ya shiga hannun jami’an Yansandan kasar Kamaru bayan ya kashe malaminsa ta hanyar caka masa wuka har sau biyu a kirjinsa.

Wannan lamari ya faru ne a ranar Talata, 14 ga watan Janairu a makarantar sakandari ta Nkolbisson dake Yaounde, babban birnin kasar Kamaru, inda dalibin ya kashe sabon malamin dake koyar dasu lissafi.

Daliban makarantar sun bayyana cewa tun a ranar Litinin aka fara samun takun saka tsakanin malamin da wannan dalibi da ba’a bayyana sunansa ba. Daliban sun ce a ranar Talata ne dalibin ya shiga aji, inda ya zabga ma malamin mari, sa’annan ya caka masa wuka a kirji.

Ba tare da wata wata ba aka garzaya da malamin zuwa asibiti, inda a can likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu, daliban sun kara da cewa duka duka malamin bai wuce watanni biyu a makarantar ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel