Ramuwar gayya: Miji yayi zina da abokiyar aikinshi bayan ya gano matarshi na kawo gardi gidanshi

Ramuwar gayya: Miji yayi zina da abokiyar aikinshi bayan ya gano matarshi na kawo gardi gidanshi

- Wani magidanci ya zargi matar shi da cin amanar shi wanda ya gano take yi a kan gadonsu

- Magidancin ya saka na'urar nadar sauti a gadonsu wanda ya tabbatar da cewa matar shi da wani gardi na morewa

- Bai yi kasa a guiwa ba ya nemi wata budurwa a wajen aikin shi wacce yake huce takaici a kanta

Wani miji da ya zargi matar shi da cin amanar shi ya hada mata tarkon da yasa ya tabbatar da hakan. Ya kama ta da wani katon gardi ne a kan gadonsu a cikin dakin aurensu.

Kamar yadda na'urar nadar sautin da mijin ya saka a cikin gadon matar ya bayyana, matar auren ta kawo kato ne wanda suke lalata dashi a dakin mijinta.

Don neman kare mutuncin shi da na matar tashi, mijin ya sakaya sunan shi da na matar tashi mai cin amanar.

"Bayan aurenmu ne na gano cewa matata na cin amanata. Na fara zarginta ne bayan da na shiga dayan dakin baccinmu naga kamar an gyara shi ne da gaggawa.

"Banda tabbacin da zai sa in tunkari matata shiyasa na aje na'urar daukar magana a wani bangare na gadonmu. Bayan kwanaki kadan ne na dauko kuma naji muryar katon da matata a na'urar.

KU KARANTA: Matar da mijinta ya ya yankewa nonuwa ta bukaci ya dawo gareta ta yafe masa

"A bayyane yake suna jin dadin lalatar da suke yi. Yana morarta fiye da yadda nake yi. Nayi tunanin abinda ya dace inyi kuma na yanke hukuncin cigaba da jin abinda suke yi na tsawon wani lokaci.

"Abinda ya bani mamaki shine yadda ta nemi mu kwanta da yammacin nan. Ai kuwa ban sassauta mata ba nayi mata komai da mugunta amma sai taji dadin hakan. Mun dade bamu ji dadin junanmu kamar haka ba.

"Amma kuma duk da haka, na samu wata a wajen aikina wacce na fara fita da ita. Zan dinga hucewa a kanta. Yarinyar gogaggiya ce, tana koya min abubuwa masu tarin yawa wanda nake gwadawa a kan matata.

"Ranar nan na sanar da matata na san tana mu'amala da wani kuma nima ina yi da wata. Munyi alkawarin ajiye hakan a matsayin sirrinmu." Cewar mijin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: