Hotunan ziyarar da Ahmed Musa da 'yan kungiyarsa suka kai wa yariman Saudiyya
Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa tare da sauran tawagarsa na Al Nassr sun kai wa yariman Saudiyya, Faisal Bin Bandar Al Saud ziyarar ban girma bayan sunyi nasarar lashe Saudi Super Cup.
Musa da 'yan tawagarsa sun doke Al Taawon da 5 -4 a bugun daga kai sai mai tsaron gida a filin wasa na Sarki Abdullah da hakan ne suka samun nasarar zama zakarun gasar kwararru na Saudiyya kamar yadda Today.ng ta ruwaito.
A yayin da suke cigaba da murnar samun nasarar zama zakarun gasar a karo na farko, tawagar sun kai wa yariman ziyarar ban girma don godiya bisa goyon bayan da ya ke basu kasancewa yana daya daga cikin masu goyon bayan kungiyar.
DUBA WANNAN: Kano: Da haramtattun kuri'u aka zabi Ganduje - Abba Gida-Gida
Wannan shine kofi na biyu da kungiyar ta zama zakara a gasar cin kofi tun bayan da Musa ya baro Leicester City ya dawo kungiyar ta yankin Larabawa.
Kungiyar ta wallafa hotunan ziyarar da suka kai wa yariman na Saudiyya a kafafen sada zumunta da suka yi wa lakabi da "Mai martaba, Yariman Saudiyya Faisal bin Bandar Al Saudi, gwamnan Riyadh ya karbi bakuncin zakarun #SaudiSuperCup."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng