Neman dawwama kan mulki: Farai minista da ministocin Putin sun yi murabus

Neman dawwama kan mulki: Farai minista da ministocin Putin sun yi murabus

Farai ministan Rasha, Dmitry Medvedev, da illahirin ministocinsa sun yi murabus bayan Shugaba Vladimir Putin ya gabatar da shirin neman yi wa kundin tsarin mulki garambawul don bashi ikon ci-gaba da kasancewa kan karagar mulki har abada.

Da ya ke jawabi a wurin taron shekara-shekara da 'yan majalisa a ranar Laraba, Putin ya gabatar da bukatar yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima ta yadda za' a karfafa ikon majalisar tare kuma da karfafa ofishin shugaban kasa.

Putin ya ce, "Ina ganin ya dace ayi kuri'a don bawa 'yan kasa damar bayyana ra'ayinsu kan gyare-gyaren kundin tsarin mulkin ƙasar."

Ya kuma nemi a yi wa kundin tsarin mulkin garambawul ta yadda za a bawa yan majalisa ikon naɗa Farai minista da ministocin gwamnati.

DUBA WANNAN: Kano: Da haramtattun kuri'u aka zabi Ganduje - Abba Gida-Gida

Ya ce, "Hakan zai ƙara wa 'yan majalisa da majalisar aiki da tabbatar da suna cin gashin kansu."

Za mu iya gina kaƙarfar Rasha ne kawai idan muna mutunta ra'ayoyin mutanen kasar.

"Idan mun haɗa kai za mu iya inganta rayuwar mutanen ƙasa. Ya zama dole Rasha ta cigaba da kasancewa jamhuriyar shugabancin kasa ƙaƙarfar."

Bayan shugaba Putin ya sanar da tsare-tsarensa, dukkan ministocinsa tare da Farai ministan kasar Dmitry Medvedev sun mika takardar su ta yin murabus.

Sa'o'i kaɗan bayan yin murabus ɗin, Putin ya naɗa Shugaba hukumar karbar haraji ta kasar, Mikhail Mishustin, Dan shekaru 53 a matsayin sabon Farai minista.

A cewar kafar yada labarai ta RIA, majalisar wakilai ta kasar za ta yi kuri'a kan Mishustin a ranar Alhamis.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel