Badakalar naira biliyan 2: Kanwar Abdulrashid Maina ta sake tsunduma shi cikin matsala
Wata kanwar Abdulrashid Maina, mutumin da ya rike mukamin shugaban kwamitin wucin gadi da ta gudanar da garambawul ga dokokin fansho a Najeriya a zamanin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ta sake kwance masa zani a cikin kasuwa.
Idan za’a tuna hukumar yaki da rashawa na EFCC tana tuhumar Maina da laifin satar makudan kudade daga asusun fanshon Najeriya da suka kai naira biliyan 2, tare da kamfaninsa Common Input Property and Investment, inda take kararsa a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja.
KU KARANTA: Gungun miyagu yan bindiga sun kai hari asibitin Zamfara, sun kashe ma’aikatan 2
Sai dai a zaman kotun na ranar Laraba, 15 ga watan Disamba, kanwar Maina, Malama Nafisat Aliyu ta gabatar da kan ta a gaban kotun, inda ta nesanta kanta daga asusun bankin da Maina ya bude da sunanta.
Nafisat ta isa kotun ne sanye da nikabi a fuskarta, sa’annan ta zauna gaba da gaba da Maina, amma dai ko kallo bai hada ta da shi ba, sa’annan ko gaisawa ba’a ga sun yi da juna ba, duk kuwa da cewa sun yi gaba da gaba bayan kammala shari’ar.
Nafisat ta ce sai bayan shekaru uku ta fahimci Maina ya bude asusun banki da sunanta ba tare da saninta ba, ta kara da cewa ta fara samun bayanan asusun bankin ne bayan wani tsohon dan hayanta, Oluwatoyin Meseke dake aiki a wani banki ya amshi takardar wutar lantarkin gidanta, ba tare da sanin abin da zai yi da shi ba.
Ta tabbatar ma kotun cewa hoton ta ne a kan asusun bankin, kuma bayanan dake asusun bankin na ta ne, amma sa hannun dake kan asusun bankin ba nata bane, haka zalika adireshin dake asusun ba adireshin gidanta bane.
Bugu da kari ta tabbatar ma kotun cewa ita ma’aikaciyar gwamnati ce ba yar kasuwa mai shigo da kaya ko fitar da su ba, sa’annan ta musanta wata masaniya kan kudi naira miliyan 231 da aka samu a asusun bankin.
Idan za’a tuna a kwanakin baya ne wata yar uwar Maina mai suna Fatima Abdullahi ta fara bayyana a gaban kotu inda ta kwance masa zani a kasuwa bayan ya yi amfani da sunanta ya bude asusun banki ba tare da saninta ba, wanda yake amfani da shi wajen boye kudaden daya sata.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng