Jerin sunaye: Tambuwal ya nada sabbin sakatarorin dindindin hudu

Jerin sunaye: Tambuwal ya nada sabbin sakatarorin dindindin hudu

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya amince da nadin sakatarorin dindindin guda hudu a ma'aikatun gwamnatin jiharsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wadanda aka yi wa nadin sun hada da Malam Abdullahi Sarkin Danko wanda a baya shine babban mai bawa gwamnan shawara na musamman a kan kafafen yada labarai da ayyukan mutane.

Sauran sun hada da Hajiya Amina Muhammad Jekada, Direkta Janar na Wuraren shakatawa na jihar mai ci yanzu, Alhaji Bandado Shehu Bandi, shugaban tsangayar zane a kwalejin ilimi ta Shehu Shagari a Sokoto da kuma Hussaini S. Gobir, wanda a baya shine direkta na Hukumar ilimin frimare na jihar.

DUBA WANNAN: Kano: Da haramtattun kuri'u aka zabi Ganduje - Abba Gida-Gida

Sanarwar da gwamatin jihar ta fitar ya ce an nada mutane hudun ne sakamakon samun guraben da ke bukatar a cike su a gwamnatin domin inganta ayyuka da jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel