Gwamna Ayade ya sake nada masu bashi shawara na musamman 90

Gwamna Ayade ya sake nada masu bashi shawara na musamman 90

Gwamna Ben Ayade ya jihar Cross Rivers ya kara nada masu bashi shawara na musamman 90 bayan 10 da ya fara nadawa tun bayan rantsar da shi kan mulki karo na biyu a watan Mayun shekarar da ta gabata.

A mulkinsa karo na farko, ya nada a kalla masu bashi shawara na musamman da hadimai 300 kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A yayin nadin hadiman, Ayade ya yi bayanin cewa yana son gwamnatinsa ta ratsa dukkan lunguna da sako na jihar ne shi yasa ya nada hadimai masu yawa.

DUBA WANNAN: Amfani 10 da kukumba ke yi a jikin dan adam

Sanarwar da hadiminsa a bangaren yada labarai, Christian Ita ya fitar ya ce gwamnan ya ce babu gudu babu ja da baya kan alkawarin da ya yi na samar wa mutanen jiharsa abinci.

A watan da ta gabata, ya rantsar da kwamishinino 4 bayan watanni bakwai da rantsar da shi mulkinsa karo na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel