Darma Mill: Gwamnati za ta samu gudumuwar harkar noma da kamfanin N20b

Darma Mill: Gwamnati za ta samu gudumuwar harkar noma da kamfanin N20b

A yunkurin taimakawa kokarin gwamnatin tarayya na inganta harkar noman shinkafa a Najeriya, Dahiru Mangal zai gina gidan aikin shinkafa.

Alhaji Dahiru Mangal zai gina wajen casar shinkafa a jiharsa ta Katsina. Wannan kamfanin casar shinkafa zai bunkasa sha’anin noman da ake yi a yankin.

A Agustan 2019 gwamnatin tarayya ta rufe iyakokinta na kasa domin ta maida hankali wajen noma, ta daina shigo da kayan abinci daga kasar waje.

Wani babban ma'aikacin wannan kamfani na Darma Mill, Mukhtar Kafinsoli, ya bayyana cewa kamfanin zai iya cashe ton 36 na shinkafa a cikin sa’a biyu.

Kafinsoli ya bayyana cewa ragowar bangaren wannan kamfanin zai kunshi rumbun ajiya. Nan ba da dadewa za a soma wannan aiki inji babban jami’in.

KU KARANTA: Za a daure wani ‘Dan Najeriya da Mai dakinsa a Turai saboda damfara

Wadannan gidajen casan shinkafa da a za a gama a karshen 2019 zuwa 2020 zai zama babu irinsu a Afrika kamar yadda Alhaji Kafinsoli ya bayyana.

Nura Dahiru Mangal wanda shi ne Darektan kamfanin ya bayyana cewa aikin zai ci Naira biliyan 20. Za kuma a dauki hayar kwararru 200 da fari.

Daga cikin kamfanin za a samu bangaren sarrafa taki da gidajen ma’aikata 120. Mutanen Indiya su ka tsara kamfanin, su ka damkawa Najeriya.

Kun san cewa Najeriya ce ta ke cin 20% na shinkafar da ake nomawa a Afrika wanda a dalilin haka gwamnatin Buhari ta yi hobbasa a noma.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel