Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun saki ma'aikatan kiwon lafiya 5 da suka sace

Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun saki ma'aikatan kiwon lafiya 5 da suka sace

Labarin da ke shigo mana da dumi-dumi na nuna cewa yan tada kayar bayan Boko Haram sun sako ma'aikatan kungiyoyin tallafin da aka sace a watan Disamban 2019 a jihar. Premium TImes ta ruwaito.

Ma'aikatan, mata biyu da maza uku sun shiga hannun yan ta'addan ne a ranar 22 ga watan Disamba yayinda yan aka budewa motarsu wuta a hanyar Monguno zuwa Damaturu.

Majiya mai karfi da aka sakaye sunansa ya bayyana cewa an sakosu ne bisa tattaunawa da hukumar DSS tayi da yan ta'addan.

Majiyar ta bayyana cewa ma;aikatan sun isa ofishin DSS dake Maiduguri misalin karfe 4 na yamma.

“It is a big day for us here in Borno with the release of the five abductees, ” the source said.

Yace: "Yau ranan farin ciki ne a Borno sakamakon sakin mutane biyar din nan. Biyu cikinsu ma'aikatan ALIMA ne, daya ma'aikacin Solidarity Int'l daya ma'aikacin IOM, na karshe kuma daga Red Cross.

Majiya bata bayyana ko an biya kudin fansa ba ko kuma wanda ya biya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel