Gobara ta tashi a dakin ajiyar gawa na babban asibitin gwamnatin tarayya Gusau

Gobara ta tashi a dakin ajiyar gawa na babban asibitin gwamnatin tarayya Gusau

Abin Allah Ya kiyaye, wani mummunan gobara ya tashi a cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya dake garin Gusau a jahar Zamfara, watau FMC Gusau, inda ta yi cinye dakin ajiyan gawarwaki mamata.

Daily Trust ta ruwaito babban likitan asibitin, Dakta Bello Muhammad Kwatarkwashi ne ya tabbatar da haka a ranar Laraba, sai dai yace basu san musabbabin tashin wutar ba, amma ya kafa kwamiti da zai gudanar da bincike domin tabbatar da dalilin gobarar.

KU KARANTA: Mace ta gari: Matar tsohon gwamnan jahar Imo ta kwantar masa da hankali a idon Duniya

Sai dai Dakta Bello yace babu gawa ko daya a cikin dakin a lokacin da gobarar ta tashi, amma dai yace ta kona komai kurmus a cikin dakin, don haka sai dai su dinga amfani da wasu dakunan ajiyan gawarwaki na wasu asibitoci dake jahar don adanan gawarwakin mamata.

Daga karshe Bello yace tuni sun sanar da gwamnatin tarayya game da aukuwar gobarar, sa’annan sun sanar da gwamnatin jahar Zamfara, haka nan kuma kwamitin da ya kafa don gudanar da binciken ta fara aikinta.

A wani labarin kuma, mutane da dama sun kone kurmus bayan wata babbar tankar dakon man fetir ta kama d wuta a kauyen Agudo dake jahar Benuwe a ranar Talata, 14 ga watan Janairu, haka zalika gidaje da dama sun kone.

Lamarin ya faru ne a kauyen Agudo yana nan ne a cikin karamar hukumar Tarka a kan babbar hanyar Makurdi zuwa Gboko, a daidai wata kwanar mutuwa, kamar yadda wani shaidan gani da ido ya tabbatar.

Shaidan mai suna Justice Anzembe ya bayyana cewa motar tankar man fetirin makare da mai tana kan hanyar ta na zuwa Gboko ne daga Makurdi, amma sai direban motar ya yi wautar bin ta cikin wasu ciyaye da ake konawa a kan hanyar, daga nan motar ta kama da wuta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel