Buhari dabbobi ya kamata yaje ya dinga mulka ba mutane ba - Deji Adeyanju

Buhari dabbobi ya kamata yaje ya dinga mulka ba mutane ba - Deji Adeyanju

- Wani mai rajin kare hakkin dan Adam mai suna Deji Adeyanju ya caccaki shugaba Buhari

- Ya ce a cikin dabbobin daji ne kadai ya kamata Buhari yayi mulki

- Adeyanju ya yabi Fani Kayode da ya dawo da dankon zumunci tsakanin shi da Mazi Nnamdi Kanu

Wani mai rajin kare hakkin dan Adam mai sun Deji Adeyanju ya kai sabon hari da caccaka kan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Deji Adeyanju ya je shafin shi na tuwita inda yayi jinjina da godiya ga Fani Kayode. Daga nan ne ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan yadda autar shi tayi amfani da jirgin shugaban kasa wajen tafiyar kanta.

KU KARANTA: Sau 6 ina karance Qur'ani, kuma na yadda Musulunci addinin zaman lafiya ne - Fasto Suleiman

Kamar yadda yace "ina so inyi amfani da wannan damar wajen mika godiyata ga Fani Kayode wanda ya kara gyara abokantaka ta da dan'uwana Mazi Nnamdi Kanu. Ina dana sanin kalubalantar shi da nayi. A cikin dabbbobin daji ne kadai Buhari ya kamata yayi mulki."

A wani bangaren kuma a jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu akan sabuwar dokar haraji a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel