Busa taba sigari: Yadda Shagari ya mutunta ofishin shugaban kasa a lokacinsa

Busa taba sigari: Yadda Shagari ya mutunta ofishin shugaban kasa a lokacinsa

Wani masani a kiyasin siyasa wanda ya samu yin jawabi a taron ‘Never Again Conference’ don tunawa da yakin basasa karo na 50 yace, Shagari mutum ne mai dabi’a ta gari, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Yace, “Na kammala makaranta. A lokacin ne mataimakin shugaban kasa marigayi Alex Ekwueme yace Shagari ya zabe ni in maye gurbin farfesa Odenigwe. A haka ne na kare a gwamnati. Idan zamu tuna, tsohon shugaban kasa Shagari ya saba shan sigari, amma baya sha a cikin mutane. Saboda mutunta ofishin shugaban kasa da yake yi, baya kuma sha a ciki.”

“Idan zai sha sigari, ya kan fito waje. Ni da Aba Dabu kan zauna mu taya shi hira. A mutumin nan ne nake ganin dan kasa nagari wanda tarihi da jaridu ba dole su samu damar dauka ba.” a cewarsa.

DUBA WANNAN: Buhari ya yi magana kan hukuncin kotun koli, ya ce nasara ce ga mutanen Imo

A yayin jawabi a wannan taron da aka yi a cibiyar MUSON da ke Onikan a Legas, sanannen mawaki Onyeka Onwenu, ya jajanta cewa ko bayan shekaru 50 da kammala yakin basa a Najeriya ake ware ‘yan kabilar Igbo a kasar nan.

Onwenu yace, “Da ilhamar da Ubangiji ya bani, nayi kokarin hada kan ‘yan Najeriya. Da ace ni mace ce Bayerabiya ko Bahaushiya, akwai yiwuwar a saurareni tare da taimakona da goyon bayana. Ina matukar fushi da Najeriya da gwamnati. Na fusata da mutanen mu. Saboda na kushe ka, kamata yayi ka tashi tsaye tare da dena korafi. Kayi abinda ya dace da kanka."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel