Abin al’ajabi: Dalibi ya sharara ma malaminsa mari, ya caka masa wuka a kirji

Abin al’ajabi: Dalibi ya sharara ma malaminsa mari, ya caka masa wuka a kirji

Ke duniya, ina za ki da mu ne? gaskiya idan da ranka ka sha kallo, a nan an samu rahoton wani dalibin sakandari ya shiga hannun bayan ya kashe malaminsa ta hanyar caka masa wuka har sau biyu a kirjinsa.

BBC ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Talata, 14 ga watan Janairu a makarantar sakandari ta Nkolbisson dake Yaounde, babban birnin kasar Kamaru, inda dalibin ya kashe sabon malamin dake koyar dasu lissafi.

KU KARANTA: Muhimman abubuwa 7 game da sabon gwamnan jahar Imo, Hope Uzodinma

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daliban makarantar sun bayyana cewa tun a ranar Litinin aka fara samun takun saka tsakanin malamin da wannan dalibi da ba’a bayyana sunansa ba.

Daliban sun ce a ranar Talata ne dalibin ya shiga aji, inda ya zabga ma malamin mari, sa’annan ya caka masa wuka a kirji.

Ba tare da wata wata ba aka garzaya da malamin zuwa asibiti, inda a can likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu, daliban sun kara da cewa duka duka malamin bai wuce watanni biyu a makarantar ba.

Sai dai tuni Yansandan kasar Kamaru suka yi awon gaba da wannan dalibi zuwa caji ofis, kuma shi ma ministan ilimin sakandari na kasar ya katse tafiyar daya kai zuwa Douala domin ya ziyarci makarantar.

A wani labari kuma, gwamnatin tarayya ta bayyana rundunar tsaro na sa kai da gamayyar gwamnatocin jahohin kudu masu yammacin Najeriya, watau yankin yarbawa suka kafa mai suna ‘Amotekun’ a matsayin haramtacciyar rundunar tsaro.

Babban lauyan gwamnati, kuma ministan sharia, Abubakar Malami ne ya bayyana haka a ranar Talata, inda yace aikin tabbatar da tsaro aiki ne na gwamnatin tarayya ita kadai.

“Kafa wani rundunar tsaro mai suna Amotekun bai halasta ba, kuma ya saba ma tanadin dokokin Najeriya, kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya samar da rundunar sojan kasa, sojan ruwa, sojan sama, Yansanda da kuma sauran hukumomin tsaro daban daban da zasu taimaka ma wajen tsaron Najeriya.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng