Farawa da iyawa: Hope Uzodinma ya bada umurnin daskare dukkan asusun gwamnatin Imo

Farawa da iyawa: Hope Uzodinma ya bada umurnin daskare dukkan asusun gwamnatin Imo

Zababben gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma, ya bada umurnin daskare dukkan asusunan gwamnatin jihar Imo daga ranar Talata, 14 ga watan Junairu, 2020.

A cikin wasikar da diraktan kamfen zababben gwamnan, Cosmos Iwu, ya saki, ya umurci dukkan bankuna da akawun gwamnatin jihar Imo, cewa kada su sake su bari gwamnatin Emeka Ihedioha ta cire kobo daya.

Wasikar ta ce an rufe asusunan daga ranar 14 ga watan Junariu, 2020.

Za ku tuna cewa a jiya Litnin, kotun koli ta fitittiki gwamna Emeka Ihedioha daga kujerar gwamna kuma ta bada umurnin rantsar da Hope Uzodinma na APC.

DUBA NAN: Yau a Tarihi: Kisan Sardauna, Tafawa Balewa, da abubuwa 2 da suka faru

Wasikar tace: "Bisa ga shari'ar kotun kolin ranar 14 ga Junairun, 2020, mai girma Sanata Hope Uzodinma, ya umurceni in sanar da ku cewa ku daskare dukkan asusunan bankin gwamnatin Imo dake bankunanku."

"Ana umurtanku kuyi biyayya ga wannan wasikar har sai lokacin mai girma gwamnan jihar Imo ya sake tuntubarku."

Mun kawo muku rahoton cewa Kotun kolin ta alanta Hope Uzodinma na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) matsayin zakaran zaben gwamnan 9 ga Maris, 2019.

Dukkan Alkalan kotun kolin sun yi ittifaki a shari'ar da Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun ta karanto cewa an zagbewa jam'iyyar APC kuri'un rumfunan zabe 388 yayinda ake tattara sakamakon zaben jihar Imo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel