PDP ta yi martani kan hukuncin koli kan zaben gwamnan Imo

PDP ta yi martani kan hukuncin koli kan zaben gwamnan Imo

Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta ce ta yi mamakin hukuncin da kotun koli ta yanke a kan zaben gwamnan jihar Imo, inda ta bayyana shi a matsayin wani mumunnan sharhi a kan tsarin demokradiyyar Najeriya kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Alkalan kotun kolin, a ranar Talata sun yi tarayya wurin yanke hukuncin soke zaben Emeka Ihedioha a matsayin gwamnan Imo inda suka bayyana Hope Uzodinma a matsayin hallastacen wanda ya lashe zaben kuma suka umurci INEC ta ba shi shaidan lashe zabe.

Alkalin guda bakwai na kotun kolin sun jadada cewa Ihedioha bai samu kuri'u mafi rinjaye ba a zaben gwamna na ranar 9 ga watan Maris.

A sakon da sakataran yadda labaranta na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar a ranar Alhamis a Abuja, ta ce PDP da 'yan Najeriya sun kasa fahimtar dalilan da kotun da dogara da su har ta kai ga zartas da hukuncin.

DUBA WANNAN: Layin waya: An maka diyar Buhari da DSS a kotu

"A gaskiya, PDP da galibin 'yan Najeriya ba su fahimci hujojji da kotun koli ta dogara da su ba har ta kai ga yanke hukuncin ta, inji shi.

Ya ce abin takaici ne yadda aka kwace wa mutanen Imo gwamnan da suka zaba kuma suka jefa wa kuri'a sannan aka mika wa jam'iyya da dan takarar da mutane ba su son su.

Mr Ologbondiyan ya ce jam'iyyar ta amince hukuncin kotun koli shine mataki na karshe kuma ya yi kira ga 'yan jam'iyyar su cigaba da hadin kai kuma su kwantar da hankulansu su saurari matakin da jam'iyyar za ta dauka kan lamarin maras dadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel