Gwamnatin tarayya ta bayyana rundunar ‘matasan tsaro na yarbawa’ a matsayin haramtacciya

Gwamnatin tarayya ta bayyana rundunar ‘matasan tsaro na yarbawa’ a matsayin haramtacciya

Gwamnatin tarayya ta bayyana rundunar tsaro na sa kai da gamayyar gwamnatocin jahohin kudu masu yammacin Najeriya, watau yankin yarbawa suka kafa mai suna ‘Amotekun’ a matsayin haramtacciyar rundunar tsaro.

Babban lauyan gwamnati, kuma ministan sharia, Abubakar Malami ne ya bayyana haka a ranar Talata, inda yace aikin tabbatar da tsaro aiki ne na gwamnatin tarayya ita kadai, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

KU KARANTA: Allah kare: Jama’a sun kone kurmus yayin da tanka makare da man fetir ta kama da wuta

Malami ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da mashawarcinsa na musamman a kan harkokin watsa labaru, Dakta Umar Gwandu ya rattafa ma hannu ya bayyana cewa kungiyar ta haramta.

“Kafa wani rundunar tsaro mai suna Amotekun bai halasta ba, kuma ya saba ma tanadin dokokin Najeriya, kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya samar da rundunar sojan kasa, sojan ruwa, sojan sama, Yansanda da kuma sauran hukumomin tsaro daban daban da zasu taimaka ma wajen tsaron Najeriya.

“Don haka babu wata jaha ita kadai ko a kungiyance dake da iko ko hurumin kafa wani rundunar tsaro da zai kare Najeriya ko kuma wani sashi na kasar, wannan kuma sashi na 45 na kundin tsarin mulkin Najeriya ne ya tabbatar da haka.” Inji shi.

A wani labarin kuma, akalla mabiyan darikar Shia na kungiyar yan uwa Musulmai, watau Islamic Movement in Nigeria, IMN, ne suka samu munana rauni a sakamakon wata arangama da suka yi da jami’an rundunar Yansandan Najeriya a Abuja.

An yi wannan dauki ba dadi ne yayin da yan shian suke gudanar da muzahara a daidai shataletalen Berger dake cikin babban birnin tarayya Abuja, inda Yansanda suka cimmasu.

Yan shian sun zanga zangar ne da nufin tilasta ma gwamnatin Najeriya sakin jagoran su, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky tare da matarsa Zeenatu, dake daure a wani gidan gyaran halayya a jahar Kaduna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel