An dawo min da hakki na - Hope Uzodinma ya yi tsokaci kan nasarar da ya samu a kotun koli

An dawo min da hakki na - Hope Uzodinma ya yi tsokaci kan nasarar da ya samu a kotun koli

Sabon gwamnan jihar Imo da kotu ta baiwa nasara a yau, Sanata Hope Uzodinma, ya ce kotu ta dawo masa da hakkinsa.

Uzodinma, wanda yayi magana ta bakin mai magana da yawunsa, Declan Emelumba, ya ce tun kafin rana irin ta yau ya kasance mai imani da Alkalan Najeriya.

Yace: "A yau, kotu mafi girma a kasar nan ta dawo mini da hakkin na da al'ummar jihar Imo suka bani."

"Hakan na nufin cewa nasarar da al'ummar jihar Imo suka bani, amma aka kwace min, ya daow. Ina mmai godiya ga Allah madaukaki,"

Emelumba ya ce sabon gwamnan zai koma jihar Imo gobe kuma zai yi jawabi ga al'ummar jihar.

Mun kawo muku rahoton cewa Kotun koli ta kwace kujerar gwamnan Imo, Emeka Ihedioha, dan jam'iyyar PDP tare da tabbatar da Hope Uzodinma, dan jam'iyyar APC a matsayin halastaccen zababben gwamnan jihar.

Kotun, mai alkalai bakwai a karkashin jagorancin alkalin alkakalai na kasa (CJN), Mohammed Tanko, ta ce ba Ihedioha ne halastaccen zababben gwamnan jihar Imo ba.

Babbar kotun, wacce ake wa lakabi da 'daga ke sai Allah ya isa', ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) data karbe shahadar cin zabe daga hannun Ihedioha tare da mika shi ga Uzodinma ba tare da wani bata lokaci ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel