Shugaba Buhari ya jajantawa kasar Nijar game da kashe-kashen da aka yi

Shugaba Buhari ya jajantawa kasar Nijar game da kashe-kashen da aka yi

A Ranar Lahadin da ta gabata ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi waya da Mahamadou Issoufou na kasar Nijar.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana da Takwaran na sa na Jamhuriyyar Nijar ne game da harin da ‘Yan ta'adda su ka kai masa.

Idan ba ku manta ba an kai wa kasar Nijar wani mumunnan hari a Garin Chinagodrar a Ranar Alhamis, 9 ga Watan Junairu, 2020.

Muhammadu Buhari na Najeriya ya yi wa Shugaban Nijar gaisuwar Allah-ya-kyauta tare da mika ta’aziyyarsa a madadin al’ummar Najeriya.

Shugaban Najeriyar ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya fitar ta bakin wani Mai magana da yawun bakinsa watau Malam Garba Shehu.

KU KARANTA: Shugaban kasa ya tsige Hafsun Soji bayan an kai harin da ya kashe mutum 160

Shugaba Buhari ya jajantawa kasar Nijar game da kashe-kashen da aka yi
Buhari ya yi alkawarin marawa kasar Nijar baya wajen fada da ‘Yan ta’adda
Asali: Facebook

Garba Shehu ya ce shugaban kasar Najeriyar ya mika sakon ta’aziyyarsa tare da jaje ga wadanda su ka rasa ‘Yanuwa da Abokan arzikinsu.

Shugaban kasar ya kuma yi Allah-wadai da wannan mugun aiki na ‘Yan ta’adda, tare da yin alkawarin ba Nijar gudumuwar yakar ta’adda.

Buhari ya kare jawabin na sa na Ranar Lahadi da jaddada cewa duk masu hannu wajen kai irin wannan hari ba su cancanci zaman lafiya ba.

A daidai wannan lokaci kuma mun ji cewa fadar shugaban kasar ta yi tir da ta’adin da wasu ‘Yan ta’adda su ka yi a Garin Mangun jihar Filato.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel