Abba Vs Ganduje: Mambobin Kwankwasiyya uku sun mutu a hatsarin mota a hanyar zuwa Abuja

Abba Vs Ganduje: Mambobin Kwankwasiyya uku sun mutu a hatsarin mota a hanyar zuwa Abuja

- Bangaren darikar Kwankwasiyya ta jam'iyyar PDP ta bayyana rasuwar mambobinta uku a hanyarsu ta zuwa kotun koli

- Sun tafka mummunan hatsari ne a hanyarsu ta zuwa Abuja a cikin Kaduna don halartar shari'a a kotun koli

- Kungiyar tayi ta'azziya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu tare da fatan mutane biyun da suka raunata zasu samu lafiya da gaggawa

Bangaren Kwankwasiyya na jam'iyyar PDP sun rasa mambobi uku sakamakon hatsarin mota da suka yi a hanyarsu ta zuwa Abuja a Kaduna.

Wasu biyu kuwa sun samu miyagun raunika kuma suna samun kulawar masana kiwon lafiya a halin yanzu.

A takardar da mataimaki na musamman a kan yada labarai na Abba Kabir Yusuf, dan takarar shugabancin jihar a karkashin jam'iyyar PDP a 2019, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya mika ga jaridar Solacebase, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Litinin da ta gabata.

DUBA WANNAN: Bayan shekaru masu yawa: Buhari ya bayyana dalilin shigarsa siyasa

"Wadanda suka rasun sune Faisal Dabo, Abba Shehe da Hassan. Wadanda suka samu raunikan kuwa sune Yahaya Muhammad da Imam," in ji takardar.

"Danginsu zasu birnesu kamar yadda addinin Islama ya tanadar a garin Kano."

Takardar tayi addu'ar samun lafiya ga wadanda suka raunatan da kuma rahamar Ubangiji ga rayukan wadanda suka rigamu gidan gaskiya.

Takardar ta kara da fatan Allah ya ba 'yan uwansu da iyalansu hakurin jure babban rashin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel