Daga karshe: Dangote ya fadi lokacin da zai siya Arsenal

Daga karshe: Dangote ya fadi lokacin da zai siya Arsenal

Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Aliko Dangote, wanda masoyin kungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ne ya bayyana niyyarsa na siyan kungiyar.

Hamshakin attajirin, ɗan shekaru 62 da arzikinsa ya ɗara fam biliyan 8.5 ya dade yana shirin karɓe kungiyar daga hannun mai kungiyar a yanzu, Stan Kroenke.

Idan ba a manta ba a baya ya taba yin alkawarin zai taya kamfanin a 2020 amma duba da cewa har yanzu bai kammala ginin matatar man sa ya dage shirin zuwa 2021.

Dangote ya yi jawabi a David Rubenstein Show cewa, "Babu shakka ina fatan in siya ƙungiyar amma abinda na dade ina faɗa shine muna da ayyukan da ke bukatar kudi dallar Amurka biliyan 20 kuma can na mayar da hankali.'

DUBA WANNAN: Ba bu matsin lambar da zai sa in saki El-Zakzaky - El-Rufai

'Ina kokarin ganin na kammala gina kamfanin toh idan mun gama a cikin 2021 zan iya siyan kungiyar.

"Ba zan siya Arsenal yanzu ba. Zan siya Arsenal ne bayan na kammala ayyukan da na fara, ina son daga kamfanin zuwa mataki na gaba ne."

A halin yanzu Arsenal ita ke mataki na 10 a Premier League bisa dukkan alamu kungiyar ta farfaɗo tun bayan nada Mikel Arteta da aka kawo ya maye gurbin Unai Emery bayan korarsa a watan Nuwamban 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel