Sarkin yawa: Manyan kasashen duniya 5 sun fara tattaun matakin da zasu dauka a kan Iran

Sarkin yawa: Manyan kasashen duniya 5 sun fara tattaun matakin da zasu dauka a kan Iran

Manyan kasashen duniya guda biyar za su gudanar da wani muhimmin taro domin tattauna matakin da ya kamata duniya ta dauka a kan gwamnatin kasar Iran biyo bayan harbo jirgin fasinjoji da ta yi.

Kamfanin dillancin labaru na Reuters ta ruwaito wadannan kasashe biyar su ne kasashen da fasinjojin jirgin da gwamnatin kasar Iran ta harbor suka fito daga cikinsu, kamar yadda ministan harkokin kasashen waje na kasar Ukraine, Vadym Prystaiko ya bayyana.

KU KARANTA: Ziyarar Osinbajo: A kullum muna maraba da zuwanka jahar Kano – Sarkin Kano

Prystaiko yace a yayin taron, kasashen za su tattauna yiwuwar biyan diyyan rai ga iyalan mamatan su 176 da suka mutu a sanadiyyar harbo jirgin da Iran ta yi, sa’annan yace zasu kaddamar da cikakken bincike game da lamarin.

“Mun kafa wannan kungiya ta ministocin kasashen wajen kasashen guda biyar dake jimamin rashin mamatansu ne. zamu taru a ranar 16 ga watan Janairu a birnin Landan domin tattauna batutuwan da suka shafi matakan sharia da kuma yadda lamarin zai kasance.” Inji shi.

A ranar Asabar din da ta gabata ne kasar Iran ta tabbatar da cewa Sojojinta ne suka baro jirgin Fasinja na kasar Ukraine bisa kuskure, inda suka kashe mutane 176 dake cikin jirgin, bayan da farko ta karyata cewa ita ta baro jirgin.

Iran dai ta harbo wannan jirgi ne bayan ta kai wasu hare haren bama bamai a sansanonin Sojojin Amurka dake birnin Baghdad na kasar Iraqi, ta kai wadannan hare hare ne a matsayin ramuwar gayyan kashe wani babban kwamandan Sojinta da Amurka ta yi.

Fasinjojin jirgin sun hada da yan kasar Iran 82, Canada 63, Ukraine 11, Sweden 10, Afghanistan 4, Germany 3 da kuma kasar Ingila 3, a yanzu dai ana cigaba da gudanar da zanga zanga a babban birnin Tehran inda jama’a ke bukatar Ayatollahi Khameini ya sauka daga kujerarsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel