Ba zan iya cika sharrudan beli ba - Maina ya koka a kotu

Ba zan iya cika sharrudan beli ba - Maina ya koka a kotu

Afam Osigwe, Lauyan Abdul Rashid Maina, tsohon shugaban kwamitin tsaftace harkan fansho ya bayyana cewa Maina fa ba zai iya cika sharrudan belin da babban kotun tarayya dake Abuja ta kakaba mai ba.

Maina na gurfana gaban kotu ne kan zargin almundahanar miliyoyin nairori da hukumar hana almundana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ke yi masa.

An gurfanar da shi tare da yaronsa, Faisal Maina.

Tuni Maina ya musanta zargin da ake masa kuma Alkali Okon Abang ya bashi belin da wasu sharruda masu tsauri.

Ga jerin sharrudan:

1. Ya gabatar da masu tsaya masa biyu kuma a tabbatar sun mallaki N500 million

2. Wajibi ne masu tsaya masa biyu su mallaki gidaje a unguwar Asokoro ko Maitama a Abuja

3. Wajibi ne masu tsaya masa su kasance Sanatoci kuma marasa kashi a gindi

4. Wajibi da Sanatocin su bayyana a kotu duk ranar da za'a zauna

5. Ya mika dukkanin takardun tafiyarsa na fasfot da sauransu

Maina ya bayyana kotu cewa duk da cewa an samu Sanatocin da suka shirya tsaya masa, basu mallaki dukiya a Asokoro ko Maitama da kotun ke bukata ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel