Gwamnonin Arewa sun taya Dahiru Bauchi alhinin rashin matarsa

Gwamnonin Arewa sun taya Dahiru Bauchi alhinin rashin matarsa

Kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya sun jajanta tare taya babban shehin Malamin darikar Tijjaniyyah, Sheikh Dahiru Bauchi alhinin rashin matarsa, Sayyada Aisha Dahiru Usman.

Daily Trust ta ruwaito kungiyar gwamnonin ta sanar da haka ne ta bakin daraktan watsa labaru na gwamnan jahar Filato, Simon Lalong, Dakta Makut Simon Macham, inda ta bayyana rasuwar Aisha a matsayin babban rashi ga iyalan malamin.

KU KARANTA: Barawo ya diro daga gidan sama mai hawa 2, ya karya wuya a jahar Imo

Gwamnonin Arewa sun taya Dahiru Bauchi alhinin rashin matrsa
Dahiru Bauchi
Asali: Facebook

“Gwamnonin Arewacin Najeriya suna taya Sheikh Dahiru Usman Bauchi alhinin rashin matarsa, muna kuma mika ta’aziyyarmu ga Shehin Malamin, iyalansa da kuma darikar Tijjaniyyah gaba daya. Fatanmu za’a tuna ta da kyawawan ayyukan da ta yi a tsawon rayuwarta na taimaka ma gajiyayyu da marasa karfi.” Inji shi.

Daga karshe Gwamna Lalong ya yi kira ga Malamin tare da Iyalansa da su dauki dangana tare da hakurin rashin da suka yi a matsayin kaddara daga Allah, sa’annan ya yi addu’ar Allah Ya kara musu hakuri, kuma ta bashi ladan juriyan rashi.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa wasu kwamitoci guda biyu da zasu sanya idanu wajen gudanar da aikin samar da wutar Mamabilla na Megawatta 3050 a jahar Taraba, yankin Arewa ta tsakiya.

Kwamitocin guda biyu sun hada da kwamitin ministoci da zasu dinga tattaunawa tare da auna matsayin aikin a karkashin jagorancin ministan wutar lantarki, da kuma kwamitin tabbatar da an gudanar da aikin yadda ya kamata tare da kammala shi a lokacin daya dace.

Kwamiti na biyu an kafa shi ne a karkashin jagorancin darakta a ma’aikatar wutar lantarki, Injiniya Faruk Yusuf, wanda zai mika rahotonsa ga minista ta hannun babban sakataren ma’aikatar, Didi Walson-Jack.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng