Matasa sun yiwa tsohon gwamnan Bauchi jifar shaidan tare da ihu barawo a kotun koli

Matasa sun yiwa tsohon gwamnan Bauchi jifar shaidan tare da ihu barawo a kotun koli

Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar, ya gamu da fushin wasu matasan da suka halarci zaman kotun kolin Najeriya yau Litinin, 13 ga watan Junairu, 2020.

Bayan zaman da kotu tayi yau, tsohon gwamnan ya fito daga cikin kotu yana daga hannunsu na gaisuwa ga mabiyansa kawai sai wasu suka fara jifansa da gorunan ruwa. Daily Trust ta ruwaito.

Yayinda jami'an tsaro sukayi awon gaba da shi gudun kada ji masa rauni, sai matasan suka bi shi suna masa ihu "Karya ne" "Barawo"

Ana kyautata zaton mabiya abokin hamayyarsa, Gwamna Bala Mohammed, suka aikata wannan aika-aikan.

DUBA NAN Jerin Shari'un gwamnonin 7 da za'a yi gobe

Mun kawo muku rahoton cewa shugaban Alkalan Najeriya, CJN Tanko Muhammad, ya dakatad da shari'ar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da abokin hamayyarsa, Abba Kabir Yusuf, na jihar Sokoto, da sauran jihohi shida zuwa ranar Talata.

Alkali Tanko Muhammad ya dawo cikin kotun bayan ya fita da farko sakamakon hayaniya da cinkoson mabiyan yan siyasan da suka cika kotun.

Daga baya kuma ya dakatad da zaman gaba daya sakamakon rashin lafiyar daya daga cikin Alkalan bakwai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel