'Yan bindiga sun saki jami'an kwastam 2 da suka yi garkuwa da su a Katsina

'Yan bindiga sun saki jami'an kwastam 2 da suka yi garkuwa da su a Katsina

'Yan bindiga a jihar Katsina sun sako jami'an kwastam biyu wadanda sukayi garkuwa dasu a ranar Laraba. An sako su ne a sa'o'in farko na ranar Lahadi zuwa hedkwata ta 17 ta rundunar sojin Najeriya.

Kamar yadda yace, an samu wannan cigaban ne bayan aikin hadin guiwa mai tsanani tsakanin Operation Hadarin Daji Da runduna ta 8 ta sojin Najeriya.

Owolabi yayi bayanin cewa an fara wannan aikin ne a kwanaki kadan da suka shude inda aka kai hari maboya da dama ta 'yan bindigar.

Wannan kokarin kamar yadda yace, anyi shi ne don tirsasa 'yan bindigar neman sulhu kuma an kashe da yawa daga cikinsu.

DUBA WANNAN: Wata sabuwa: Shehu Sani ya kara fada wa 'tsaka mai wuya' a hannun hukumar EFCC

"Wasu daga cikin shugabannin 'yan bindigar sun tura sako ga babban kwamandan runduna ta 8 din ta sojin Najeriyan dake kula da Katsina Da Zamfara, a kan bukatarsu ta rungumar zaman lafiya ba tare da sun saka sharadi ba," cewar Owolabi.

"Rundunar sojin zata cigaba da tabbatar da ta kwace makamai kafin ta yadda da yarjejeniyar zaman lafiya kamar yadda wasu jihohin Arewa maso yamma suka amince," ya kara da cewa.

A halin yanzu, rundunar sojin ta cigaba da aiki kamar yadda kwamandan ya bada umarni don shafe duk yankunan da 'yan bindigar ke da sansani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel