Sai bayan shekara daya da mutuwar mijina aka sanar dani - Matar soja

Sai bayan shekara daya da mutuwar mijina aka sanar dani - Matar soja

A ranar jajiberin sabuwar shekara ne yayin da miliyoyin mutane suke murnar sabuwar shekara, gidan Abdulazeez Musa wanda jami'i ne a rundunar sojin Najeriya suka fada halin tashin hankali.

A wannan ranar ne rundunar sojin Najeriya ta sanar musu da rasuwar sojan mai shekaru 35 a duniya, a yayin yakar 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.

An gano cewa Musa mai lambar aiki 14NA/71/1222, na bangaren samarwa da sufuri ne na rundunar sojin Najeriya.

Kafin su samu labarin mai matukar girgiza zuciya, an gano cewa danginsa sun dena samunsa a waya tun a watan Disamba na 2018, lamarin da ya jefa matarsa da diyarsa mai shekaru hudu cikin tsananin rudani.

Danginsa sun dena samunsa a waya ne tun bayan da mayakan Boko haram suka kai hari bataliya ta 157 dake Metele a Arewacin Borno a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2018 a yayin da 'yan ta'addan suka kashe sojoji masu yawa.

Amma kuma a wancan lokacin, rundunar sojin ta musanta mutuwar sama da sojoji 100 a harin amma sai ta tabbatar da mutuwar 23.

DUBA WANNAN: Dandalin sada zumunta: An yi 'caa' a kan Buhari bayan ganin takalmansa 'futu-futu' da kura yayin taro a Villa (Hotuna)

A takardar da shugaban sojin Najeriya, Lt Gen Tukur Buratai ya fitar kuma Brig Gen Sani Usman yasa hannu, ta tabbatar da cewa sojojin 12 ne kadai suka mutu a Kukawa, Ngoshe, Kareto da Gajiram duk a jihar Borno bayan harin da aka kai tsakanin 2 zuwa 17 ga watan Nuwamba, 2018.

Bayan wannan harin, matar Musa mai suna Sherifat tayi kokarin samunsa ta waya amma shiru. Bayan nan ne tace sun tuntubi wani babban sojan da ya sanar dasu cewa komai lafiya kuma Musa na cikin koshin lafiya.

"A ranar 31 ga watan Disamba 2019 ne aka tuntubi dan uwan Musa wanda shine magajinsa kuma aka sanr dashi cewa Musa ya riga mu gidan gaskiya. Sun ce an kasheshi ne tun a harin da aka kai musu na watan Nuwamba 2018." in ji mai takabar.

Musa wanda ya fito daga jihar Kwara, ya shiga soja ne tun a 2014, shekara daya bayan ya auri Sherifat, wacce take dauke da ciki a lokacin da ya tafi horarwa. Musa ya dawo a matsayin sojan Najeriya bayan matarsa ta haifa diya mace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel