Giwa ta fadi: Wani tsohon gwamna na kwance da shanyewar barin jiki, yana neman kudin magani

Giwa ta fadi: Wani tsohon gwamna na kwance da shanyewar barin jiki, yana neman kudin magani

- Tsohon gwamna Dr. Victor Olunloyo na kwance bashi da lafiya inda yake fama da shanyewar barin jiki

- Bayan tsananin rashin lafiyar na shi, gwamnan ya 'fada kwata' ta yadda dubbai kalilan suke da matukar muhimmanci garesa

- Rashin kudin magani da kuma halin ko in kula da gwamnatin jihar ta nuna masa ce ta sanya kullum rashin lafiyar ke cigaba

Wannan lokacin na daya daga cikin lokutan jarabawa da tsohon gwamnan jihar Oyo, Dr. Victor Olunloyo yake fuskanta. An gano cewa tsohon gwamnan jihar Oyo din na kwance a gidansa dake Ibadan inda yake fama da shanyewar barin jiki. Kuma babban kalubalensa a halin yanzu shine rashin kudin siyan magunguna, kamar yadda jaridar Polis Online ta ruwaito.

An gano cewa tsohon gwamnan ya 'fada kwata' ta yadda dubbai kadan suke da matukar muhimmanci garesa. An gano cewa rashin lafiyarsa na kara ta'azzara ne sakamakon 'halin-ko-in-kula' da gwamnatocin jihar da suka gabata suke nuna masa.

DUBA WANNAN: Ribadu ya hada kan Tinubu, Obasanjo, Atiku da sauransu

Binciken Sentry ya bayyana cewa gwamnatin mulkin tsohon gwamna Abiola Ajimobi ta nuna masa kulawa, har zuwa lokacin da suka samu rashin jituwar siyasa da matar Olunloyo, Ronke.

Sakamakon ta'azzarar rashin lafiyar tsohon gwamnan, wani farfesan Najeriya dake zama a UK ya samu zantawa da wani jigo a gwamnatin Seyi Makinde don taimakawa. Amma kuma sai jami'in, wanda tsohon dan majalisar jihar ne yaki jawo hankalin gwamnan a kan halin da tsohon gwamnan ke ciki.

An gano cewa, tsohon dan majalisar ya fusata da Olunloyo ne saboda bai tsaya masa ba a lokacin da ya bukacesa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: