Yanzu-yanzu: Sojoji sun kai sumame maboyar 'yan Boko Haram, sun ceto mutane

Yanzu-yanzu: Sojoji sun kai sumame maboyar 'yan Boko Haram, sun ceto mutane

Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarun ta sun kai sumame mafakar 'yan ta'adda kuma sun ceto mutane biyar ciki har da dattijo mai shekaru 80, mata uku da karamin yaro a jihar Borno a cikin 'yan kwanakin da suka gabata.

Jami'in yada labarai na rundunar, Kwanel Aminu Iliyasu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Abuja.

Iliyasu ya bayyana cewa dakarun bataliya ta 121 a Pulka a karamar hukumar Gwoza sun lalata mafakar 'yan ta'adda da ke dutsen Zeledva a hanyar Pulka-Bokko-Ngoshe a ranar Laraba.

Sanawar ta ce: "A ranar 7 ga watan Janairu, dakarun bataliya ta 121 da ke Pulka a karamar hukumar Gwoza yayin Operation RUFE KOFA sun tarwatsa mafakar Boko Haram da ke dutsen Zeledva a hanyar Pulka-Bokko-Ngoshe."

Ya kara da cewa dakarun hadin gwiwa ta bataliya 192 a Gwoza tare da Dakarun tsaro na Kamaru da Civilian Joint Task Force da mahauta sun hau dutsen Ungwan-Gara-Kwatara inda 'yan ta'adda ke buya.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe sojan saman Najeriya a Kaduna

A cewarsa' yan ta'addan sun tsere bayan sun hango sojojin amma duk da haka sojojin sun karasa sun lalata mafakar.

Ya ce: "A yayin sumamen, sojojin sun ceto mutane 5 da 'yan ta'addan suka bari ciki har da dattijo mai shekaru 80 da mata uku da karamin yaro daya.

"Yayin wani sumamen kuma da dakarun 21 Special Brigade da ke Bama su kayi a ranar 9 ga watan Janairu, sun gano sassan jikin wani dan ta'adda da aka kashe yayin musayar wuta da kuma bindiga kirar AK47.

"A ranar 8 ga watan Janairu, dakarun bataliya ta 112 da ke karamar hukumar Mafa sun yi wa 'yan Boko Haram luguden wuta sun kwato AK47 guda da bandolier ta 7.62mm NATO.

"Sauran kayayakin da suka kwato sun hada da AK47 da aka dura wa harsashi 7.62mm ta musamman inda ake ganin wasu kuma sun tsere da raunukan bindiga daban-daban.

"A wani karawa da da su kayi da 'yan Boko Haram a ranar 6 ga watan Janairu, dakarun 22 Brigade da ke Dikwa sun ceto wani Mr Ibrahim da 'yan ta'addan suka yi garkuwa da shi a baya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel