Matar Buhari da 'ya'yansa na da 'yancin amfani da jirgin shugaban kasa - Garba Shehu

Matar Buhari da 'ya'yansa na da 'yancin amfani da jirgin shugaban kasa - Garba Shehu

Fadar shugaban kasa ta ce matar shugaban kasa da ‘ya’yansa suna iya amfani da jirgin saman fadar shugaban kasar idan bukatar hakan ta taso.

Babban mai bada shawara ta musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan yada labarai, Garba Shehu ne ya sanar da hakan a sakon da ya tura wa jaridar The Punch a ranar Asabar.

Shehu ya mayar da martani ne a kan cewa Hanan Buhari ta je jihar Bauchi daukar hoto da jirgin fadar shugaban kasar.

Mai magana da yawun shugaban kasar yace Hanan ta mika bukatar ta ne gaban shugaban kasar kuma ya amince da hakan bayan ya sanar da mai bada shawara a kan tsaron kasa.

Shehu yace, “Da gaske ne an kai daya daga cikin iyalan shugaban kasa jihar Bauchi a jiya don aikin kanta. Ba tafiya ce wacce bata dace ba. Fadar shugaban kasar ta sanar da shugaban tsaron kasa wanda ya sanar da kungiyar matuka jirgin saman fadar.”

DUBA WANNAN: Gwamna Mohammed ya dakatar da shugabannin kananan hukumomi 2, ya bada dalili

“A al’adance, iyalan shugaban kasar na da damar amfani da jirgin tare da wasu mutane hudu. Mutane hudun sun hada da mataimakin shugaban kasa, shugaban majalisar dattijai da kuma wasu mutane biyu." cewar Shehu.

Idan bamu manta ba, mutane sunyi caa a kan shugaban kasar a kan barin diyarsa da yayi taje jihar Bauchi da jirgin fadar don amfanin kanta.

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, Hanan ta kai ziyara jihar Bauchi ne don halartar hawan daba da fadar ta shirya.

A cikin kwanakin nan ne diyar shugaban kasar ta kammala digirinta a wata jami’a dake London inda ta kammala da digiri mai daraja ta farko a fannin daukar hoto. An gano cewa sarkin Bauchi ne ya gayyaceta a matsayin bakuwa ta musamman.

A hotunan da tuni suka yawaita a kafafen sada zumuntar zamani, an ga Hanan na sauka daga jirgin sama kuma jami’an gwamnatin jihar Bauchi sun karbeta hannu bibbiyu.

An kara gano cewa, hawan daba din an shirya shi ne na musamman saboda diyar shugaban kasar don ta dauka hotunan al’aadu, yanayin gine-ginen gargajiya da sauran wuraren tarihi na jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel