Za a fara samun wutan lantarki na sa'o'i 18 a kullum - Ministan Makamashi

Za a fara samun wutan lantarki na sa'o'i 18 a kullum - Ministan Makamashi

Ministan makamashi , Injiniya Sale Mamman ya ce nan ba da dadewa ba 'yan Najeriya za su fara morar wutar lantarki na tsawon sa'o'i 18 a kowanne ranar da zarar wutar da aka samarwa da labarwa ta kai megawatts 7,000.

Ministan ya bawa 'yan Najeriya tabbacin cewa za su ga cigaba a yanayin samun wutan lantarki a kasar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Injiniya Mamman ya bayar da tabbacin cewa: "A bangaren gwamnati, muna kokarin inganta ayyuka ta hanyar fadadawa kuma na ce zuwa karshen shekara za mu samu megawatta 7,000.

"Idan muka samu hakan, akwai yiwuwar za mu rika samun wutan lantarki na sa'o'i 18 a kullum kuma da zarar mun samu megawatt 11,000, kowa zai samu wadacen wutan lantarki."

An kan batun karin kudin lantarki, ministan ya ce kamfanonin rarraba lantarkin da hukumar kula da lantarki na kasa, NERC, sun ratabba hannu kan wata yarjejeniya.

DUBA WANNAN: Sunaye: BUK ta daga darajar lakcarori 15 zuwa Farfesa

Ya ce, "Yanzu abin ya fita daga hannun gwamnati, kashi 60 cikin 100 yana hannun 'yan kasuwa ne amma mu ke sa ido a kan yadda suke ayyukansu. Kawai za mu tabbatar an inganta lamarin ne kamar yadda ya ke a wasu kasashe. Muna gayyatan masu son saka hannun jari su zo amma idan ta mu tsara farashin ba ba za su zo ba."

Ministan ya ce aikin fadada wa da sauya-sauye da ake yi zai bawa kamfanonin rarraba lantarkin daman aiki yadda ya kamata, inda ya ce ba zai yi wa gwamnatin tarayya ta cigaba da saka hannu a harkar ba.

Ministan ya ce: "A 2018, gwamnatin tarayya ta bayar da N700bn don cike gibin da ke tsakanin masu samar da lantarki (GenCos) da masu rabar da lantarki (DisCos) saboda GenCos za su biya kudin gas. Ba zai yi wu mu cigaba da hakan ba domin a bara mun karbi N600bn don cike wani gibin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel