Tashin hankali: Kyakkyawar budurwa ta kashe kanta saboda ta rasa masoya a dandalin Instagram

Tashin hankali: Kyakkyawar budurwa ta kashe kanta saboda ta rasa masoya a dandalin Instagram

- Wata matashiyar budurwa mai shekaru 19 ta kashe kanta bayan da ta kasa samun 'likes' isassu a kafafen sada zumuntar zamani

- Chloe Davison na da burin zama 'model' ne shiyasa ta dogara da kafafen sada zumuntar zamani

- Ta kashe kanta ne ta hanyar rataya a dakin baccinta

Wata matashiyar budurwa ta kashe kanta bayan ta kasa samun isassun masoya a hotunanta da take wallafawa a kafafen sada zumuntar zamani.

Chloe Davison mai shekaru 19 a duniya tana da burin zama 'model' ne kuma ta dogara da kafafen sada zumuntar zamani, kamar yadda yayarta mai suna Jade ta sanar.

"A tunaninta bata kai ba tunda bata samun isassun masoya da masu tsokaci a kan hotunanta," yayarta mai shekaru 20 ta ce.

Matashiyar mai matukar son daukar hoton selfie a dakin baccinta ta sagale kanta ne yayin da take hira a kafar sada zumuntar zamani.

Tun bayan da ta fara amfani da kafar sada zumuntar zamani a shekarun da suka gabata, maganarta kullum shi ne masoyan hotunan ta nawa ne, mahaifiyarta Clair Reynolds mai shekaru 44 ta ce.

"Tayi mugun sabo da manhajoji kamar su Instagram da Snapchat," cewar Nick Coombs mai shekaru 55 wanda ya san Chloe tun tana karama.

KU KARANTA: Kwamacala: Wata mata ta haifi tagwaye wanda kowanne ubansa daban

"Tana daukar sa'o'i da yawa wajen daukar hoto amma zata goge shi, matukar mutane basu nuna suna so ba," Coombs ya kara da cewa.

Chloe bata mu'amala da mutane kuma bata ziyarar kawaye. A maimakon haka kullum tana faman daukar hoto ne don sanyawa a kafafen sada zumuntar zamani.

Sau da yawa ma'abota amfani da kafafen sada zumuntar zamani kan yi mata ba'a. Idan hakan ta faru, ta kan kasa bacci tayi ta kuka tsawon daren.

A ranar Juma'a ne mahaifiyarta da yayarta suka iske ta a sagale a dakin baccinta. Mahaifiyarta ta dora wa kafafen sada zumuntar zamani laifi a kan kisan da 'yarta tayi wa kanta. Tace Chloe kyakyawa ce, ita ce dai bata gani kuma ta dogara da abinda mutane ke cewa a kanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel