Yanzu-yanzu: Boko Haram sun yi wa mutum uku yankan rago, sun kuma awon gaba da bakwai

Yanzu-yanzu: Boko Haram sun yi wa mutum uku yankan rago, sun kuma awon gaba da bakwai

Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun yi wa mutane uku yankan rago tare da sace wasu bakwai a yayin da suka yi kwanton bauna a babban titin Maiduguri zuwa Damataru.

The Punch ta ruwaito cewa wata majiya daga jami'an tsaro da ta nemi a boye sunan ta ta ce lamarin ya faru ne a tsakanin Jakana da Auno kimanin karfe 11.50 na safiyar ranar Alhamis.

An shaidawa majiyar Legit.ng cewa an yi wa mutane uku yankan rago kuma an bar gawarwakin su a gefen babban titi kusa da Auno.

An kuma gano cewa 'yan ta'addan sun yi awon gaba da mutane bakwai da karfi da yaji bayan kashe mutane ukun.

Wani dan kungiyar direbobi na kasa (NURTW) da ke aiki a wata tashan mota na jiha da ya nemi a boye sunansa ya tabbatar da rahoton kuma ya ce wasu direbobin da ke bin hanyar sun ajiye motocinsu domin tsoron hari.

DUBA WANNAN: Hankula sun tashi bayan an gano gawar dan kwallo da kifi suka cinye a teku

The Punch ta ruwaito cewa babban titin Maiduguri-Damaturu da a baya shine hanya guda mai lafiya na shiga garin Maiduguri shima yanzu ya yi kaurin suna cikin 'yan kwanakin nan da satar mutane farar hula da sojoji.

A cikin makon nan, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara ya yi musayar kalmomi da sojoji kan yunkurin da sojojin su kayi na korar wasu mutane daga kauyukan Jakana da Mainok.

A cikin makon nan, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara ya yi musayar kalmomi da sojoji kan yunkurin da sojojin su kayi na korar wasu mutane daga kauyukan Jakana da Mainok.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel