Hankula sun tashi bayan an gano gawar dan kwallo da kifi suka cinye a teku

Hankula sun tashi bayan an gano gawar dan kwallo da kifi suka cinye a teku

Wata tawagar masu binciken karkashin ruwa sun gano gawar Eric Birighitti bayan manyan kifaye wato Shark sunyi cinye sassan jikinsa a kasan teku Australia.

Tawagar masu binciken ainihi suna neman wani mai binciken karkashin ruwa ne da matarsa da wani kifin teku mai hatsari ya kai wa hari.

Amma sai aka gano cewa gawar Birighitti ne wanda dan asalin Peth ne kifayen uku suka cinye bayan kammala bincike.

Matashin dan kwallon mai shekaru 21 a duniya ya tafi hutu ne tare da abokansa inda ya sulube ya fada cikin teku yayin da ya ke tafiya a kan duwatsu.

DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana makomar El-Zakzaky

Daga nan ruwa ya yi awon gaba da shi yayin da abokansa suka yi kokarin taimaka masa amma ba suyi nasara ba.

Kafin rasuwarsa, an dauki nauyinsa ya buga wasan kwallon kafa da ya ke matukar sha'awa a Hasting Broncos a Kwallejin Hasting da Kwallejin St Thomas Aquina da ke New York.

Kungiyar ta Hasting Broncos ta yi ta'aziyya ga matashin inda ta rubuta cewa ta yi matukar bakin cikin samun labarin rasuwar Eric Birighitti.

Eric Birighitti ya buga wa Hastings wasa a 2016 da 2017 inda ya lashe kambu na kasa tare da tawagarsa.

Kungiyar ta ce za ta yi kewarsa sosai kuma ta mika ta'aziyya ga iyalansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel