An kama mutumin da ya yi barazanar kashe Trump kan kisan Soleimani

An kama mutumin da ya yi barazanar kashe Trump kan kisan Soleimani

An kama wani mutum dan jihar Florida da ya yi barazanar kashe Shugaba Donald Trump na Amurka saboda kashe babban kwamandan Sojojin Iran, Qassem Soleimani.

Chauncy Lump mai shekaru 26 mai aikin daga Fort Launderdale ya yi bidiyo kai tsaye a Facebook a ƙarshen mako inda ya yi barazanar kashe shugaban Amurka a matsayin daukan fansa kan harin da Amurka ta kai da ya yi sanadin mutuwar Soleimani.

A yayin da ya ke naɗan bidiyon Lump ya yi barazanar da dama ciki har da cewa "Ya kashe shugaba na, ku faɗa min inda Donald Trump ya ke da kuma cewa "Dole in gano inda Donald Trump ya ke saboda idan ban gano inda ya ke ba zan tarwatsa Broward County." Lump ya nuna bindiga ƙirar AK 47 a bidiyon.

Agent Lucas ya rubuta cewa jim kaɗan bayan Trump ya sanar cewa Amurka ta kashe Soleimani a Iraqi a matsayin fansa na kai hare-haren ta'addanci. Lump ya fara naɗan bidiyonsa kai tsaye da sunan "Blackman vs America" a Facebook. A cikin bidiyon Agent Lucas ya ce Lump ya yi barazanar kashe shugaban kasar da ke gidan hutuwa na Mara-a-Lago nisan sa'a daya a mota daga inda ya ke.

DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana makomar El-Zakzaky

Da aka tunkare shi kan barazanar a safiyar Lahadi a gidansa, Lump ya amsa cewa shine ya yi bidiyon a matsayin martani kan mutuwar Soleimani amma ya yi ne kawai don ba'a inda ya yi nadamar cewa "da na sani bai yi hakan ba tunda farko", kamar yadda White ya rubuta.

A halin yanzu ana tuhumar mai gadin da aikata babban laifi na barazanar kashe shugaban ƙasa kuma aka ajiye shi gidan gyaran hali a ranar Alhamis har sai ya bayar da jingina ta $100,000 kamar yadda takardun kotu suka nuna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel