Shugaban kwamitin karbar mulki ya yanke jiki ya fadi mattace bayan kammala taro a Abia

Shugaban kwamitin karbar mulki ya yanke jiki ya fadi mattace bayan kammala taro a Abia

Shugaban kwamitin karbar mulki na karamar hukumar Arochukwu a jihar Abia, Mr Onyekachi Okoro ya mutu kamar yadda wani jigo a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a yankin ya tabbatar.

An ruwaito cewa Okoro ya yanke jiki ya fadi ne a wani gida da ke Umuahia a misalin karfe 1 na ranar Alhamis kuma ya ce ga garin ku kafin a kai shi asibiti.

Shugaban jam'iyyar PDP, Mr Anthony Nwanko, ne tabbatar wa manema labarai rasuwar a Cibiyar Lafiya ta tarayya da ke Umuahia inda aka kai marigayin domin likitoci su duba shi.

Nwankwo, wanda amini ne ga marigayin dan siyasan ya ce ya yanke jiki ya fadi ne bayan an kamalla wani taro da wasu jami'an karamar hukuma a Umuahia.

Ya ce, "Mutumin ya yi taro da shugaban ma'aikata da ma'ajin karamar hukuma a Umuahia.

"Bayan haka, he ziyarci shugaban mu (da ba a bayyana sunansa ba). A gidansa, ya shiga ban daki.

"Bayan ya fito daga ban dakin sai ya fara jin jikinsa ya canja kuma ya yanke jiki ya fadi," inda ya kara da cewa an garzaya da shi zuwa asibiti nan take."

DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana makomar El-Zakzaky

Ya kara da cewa an tuntubi shugaban asibitin, Dr Azubike Onyebuchi da wasu likitocin nan take domin su kai taimaka su farfado da shi.

Ya karyata wasu rahotanni da suka ce marigayin ya yanke jiki ya fadi ne a gidansa a Arochukwu bayan taron da aka yi a gidansa da wasu jami'ai.

Wani likita a sashin kula da wadanda suka yi hatsari da masu bukatar taimakon gaggawa da ya nemi a sakayya sunansa ya ce ko da aka kawo mutumin asibiti ya riga ya mutu.

Kamfanin dillancin labarai (NAN) ta ruwaito cewa gawarsa yana can asibitin a lokacin rubuta wannan rahoton.

An nada Okoro a matsayin shugaban karamar hukuma ne a watan Disambar 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel